rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Fina-Finai Kano

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

MOPPAN zata duba bukatar da Rahama Sadau ta mika mata

media
Fitacciyar Jarumar Fina-finan Hausa Rahama Sadau. YouTube

Fitacciyar Jarumar masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood Rahama Sadau, ta nemi afuwar hadaddiyar kungiyar masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finan Hausa, MOPPAN, tare da neman kungiyar ta bata damar cigaba da haskawa a masana’antar.


Fitacciyar Jarumar ta nemi afuwar ce ta hanyar rubuta wasika zuwa ga shugabancin kungiyar ta MOPPAN, kamar yadda shaidar gani da ido, wato Jaridar Premium Times da ake wallafawa a Najeriya ta rawaito.

Yayin da yake amsa tambayar ko zasu amince da bukatar Jarumar, sakataren kungiyar ta MOPPAN Salisu Mohammed, ya ce zasu yi taro a ranar Juma’a 27 ga watan Oktoba, domin duba matakin da cancanta su dauka.

Idana za’a iya tunawa, a ranar 3 ga watan Oktoban shekara ta 2016, Hadaddiyar kungiyar ta masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finan Hausa, MOPPAN ta dakatar da Rahama Sadau daga haskawa a fina-finan Hausa, sakamakon bidiyon wakar da yi, dawani mawaki Classiq, da suke rugumar juna.