
Muhimman labaran masana'antun shirya Fina-finai na Kannywood, Nollywood da Bollywood
Shirin dandalin Fasahar Fina-finai wanda Hauwa Kabir ke gabatarwa, shirin na wannan makon zai baku labarin yadda wasu 'yan fim suka dade a gidan aure, bayan wata shiri da ya tada hankalin masu saurare kan mutuwar auren wasu 'yan fim din har su 7. Kan haka wasu taurarin Kannywood ma'aurata su kayi tsokaci a kai.