Isa ga babban shafi
Isra'ila

Isra'ila ta kai harin sama kan Falasdinawa a Gaza

Rundunar Isra’ila ta yi amfani da tankar yaki da jiragen sama wajen kai farmaki kan wurare uku na Hamas a zirin Gaza bayan ta zargi Falasdinawa da yunkurin kai harin bindiga kan sojojinta a yau Juma’a.

Akalla Falasdinawa 12 aka kashe tun bayan barkewar rikici tsakaninsu da sojin Isra'ila a kan iyakar Gaza da Isra'ila
Akalla Falasdinawa 12 aka kashe tun bayan barkewar rikici tsakaninsu da sojin Isra'ila a kan iyakar Gaza da Isra'ila REUTERS/Ibraheem Abu Mustafa
Talla

Wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce, dakarunta sun mayar da martanin ne akan iyakar Gaza da Isra'ila amma babu mutun ko guda da ya jikkata ballantana rasa ransa.

Wannan dai na zuwa ne bayan kwana guda da Faladinawa suka kaddamar da gagarumar zanga-zanga a zirin Gaza, lamarin da ya haddasa rikicin da ya kai ga rasa rayukan Falasdinawa 12 kamar yadda hukumomin Gaza suka sanar.

Sojojin na Isra’ila sun yi amfani da harsashai na gaske kan mutanen Gaza da suka ce, sun kusanci katangar iyakar Isra'ila da Gaza tare da jifan su da duwarwatsu da kuma aci-bal-bal.

Dubban Falasdinawa ne dai suka shiga zanga-zangar, in da suke bukatar a ba su damar komawa kasar da kakanninsu suka fice daga cikinta a lokacin yakin 1948, in da a yanzu aka shigar da kasar cikin Isra’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.