Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinawa

Kwamitin Sulhu zai zauna don tattauna rikicin Isra'ila da Gaza

Minista a ma’aikatar tara bayanan sirri na Isra’ila  Yisrael Katz ya musanta bayanan da ke cewa sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta da kungiyoyin da ke dauke da makamai a yankin Gaza na Palasdinu.

Musayar wuta tsakanin Isra'ila da mayaka a yankin Gaza na Palasdinu
Musayar wuta tsakanin Isra'ila da mayaka a yankin Gaza na Palasdinu REUTERS/Suhaib Salem
Talla

Isra’ila ta sanar da kai hare-hare akan wurare sama da 60 a cikin sa-o-i 24 da suka gabata a yankin na Gaza, abinda ta kira mayar da martani sakamakon hare-hare da makamai masu linzame da aka harba daga yankin, lamarin da ya jefa bangarorin biyu a cikin yanayin fito-na-fito mafi muni a cikin shekaru 4.

Wani lokaci a wannan laraba ake sa ran Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da zama na musamman domin tattaunawa dangane da wannan sabon rikici da ya barke tsakanin bangarorin biyu.

Kasar Kuwait ta raba wa wakilan Kwamitin Tsaron da wani daftari kafin taron da ke neman daukar matakan bai wa Palasdinawa kariya daga hare-haren na Isra’ila, yayin da jakadiyar Amurka a Majalisar Nikki Haley, ta ce ya zama wajibi ‘’Kwamitin Tsaron ya dauki mataki sakamakon hare-haren da ake kai wa Yahudawa fararen hula da ba su aikata wani laifi ba’’ a cewarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.