Isa ga babban shafi
Sauyin yanayi

Times ta karrama Greta Thunberg

Mujallar Times ta bai wa matashiya Greta Thunberg lambar yabo ta gwarzuwar shekara sakamakon jarumtar da ta nuna wajen fafutukar ganin shugabanni sun dauki matakan yaki da dumamar yanayi a duniya.

Greta Thunberg
Greta Thunberg REUTERS/Javier Barbancho
Talla

Thunberg ‘yar Sweden mai shekaru 16 ta yi rawar gani ne bayan da ta ja daga tare da kalubalantar halin da duniya ke ciki sanadiyyar rashin daukar matakai kan matsalar dumamar yanayi, inda ta jagoranci wani gangami zuwa Majalisar kasar cikin watan Agustan 2018.

Thunberg ba tare da taimakon wata kungiyar masu fafutuka ba, ta gabatar da mabanbantan gangami don nuna bacin rai kan halin ko-in-kula da mahukunta ke nunawa kan matsalar dumamar yanayi.

A wata zantawarta da mujallar Times gabanin sanar da ita a matsayin gwarzuwar shekara ta bana, matashiyar ‘yar faftukar ta ce, bai kamata a rika rayuwa kamar babu gobe ba, kamata ya yi a dauki matakan da za su gyara rayuwar yau da ta gobe, maimakon barin ‘yan baya a cikin matsala.

Yayin wani gangamin wayar da kai da Thunberg ta faro daga Amurka zuwa kasashen nahiyar Turai da arewacin Amurka har ma da Canada ta ce, abin kunya ya kare ga duk shugaban da ya gaza bayar da gudunmawa wajen magance matsalar dumamar yanayi.

An dai sanar da nasarar Thunberg ne a matsayin gwarzuwar shekarar ta Mujallar Times a ranar Laraba, a daidai lokacin da matashiyar ke halarta taron yanayi a Spain, inda nan ma ta ke kalubalantar shugabannin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.