rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gobara a makarantar Islamiyya ta kashe yara 26

Wata gobara da ta tashi a makarantar Islamiyya a kusa da babban birnin Liberia, Monrovia, cikin daren Talata ta yi sanadin mutuwar dalibai 26 da malamansu biyu,kamar yadda wata sanarwa daga gwamnatin kasar ta bayyana.

Hukumar agaji ta kasar ta shaidawa shugaba George Weah cewa mutane 28 suka salwanta a gobarar,kuma tuni shugaban ya ziyarci inda al'amarin ya auku.