rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gobarar dajin Amazon ta dauki hankalin taron G7

Gobarar dake kone daji mafi girma a duniya na Amazon na ci gaba da daukar hankali a taron kasashen G7 masu karfin tattalin arziki da ke gudana a Faransa, bayan da rahotanni daga Brazil suka ce an samu tashin karin gobarar a sassan Amazon da a yanzu adadinsu ya haura dubu tara. Dajin na Amazon dake bangaren arewacin Brazil, shi ne daji mafi girma a duniya, la’akari da cewa yana da fadin sama da murabba’in kilomita miliyan 5, da ya ratsa ta cikin kasashe 9, inda daga nan ne kuma masana kimiya suka ce duniya ke samun kashi 1 bisa 5 na iskar Oxygen da dan adam ke shaka.