rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gwamnatin Zamfara ta tsige masu rike da Sarautun Gargajiya 4

Gwamnatin Jihar Zamfara dake Najeriya ta sanar tube wasu masu rike da Sarautun Gargajiya 4 daga mukaman su, saboda zargin da ake musu na hada baki da masu aikata laifufuka ana cutar jama’a. Kwamishinan kananan hukumomi ya tabbatar da haka, inda yace daya daga cikin wadanda ake zargi yayi batan dabo, kuma ana cigaba da neman sa.