rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gwamnoni basu da cikakken iko akan jami'an tsaron da ke Jihohinsu - Abdul'aziz Yari

Gwamnan jihar Zamfara, kuma shugaban kungiyar gwamnoni ta Najeriya, Abdul-Aziz Yari Abubakar, ya bukaci majalisun tarayyar kasar da su cire wa gwamnoni mukamin da aka lakaba musu na shugabannin jami’an tsaron jihohinsu. Yari ya ce gwamnonin basu da bukatar wannan mukami la’akari da cewa basu da cikakken ikon sarrafa jami’an tsaron da ke jihohinsu, ta hanyar hukuntawa, kora ko kuma daukar sabbin jami’an tsaron, duk da cewa suna amsa mukamin shugabannin jami’an tsaron jihohin na su.