Isa ga babban shafi
Rwanda

Furofesan shari’a, Ba’amurke Peter Erlinder yace an so a batar da shi ne a Rwanda

Furofesa a fannin shari’a, Ba’amurke Peter Erlinder wanda ya yi zaman gidan-yari na tsawon mako uku a Rwanda, kan ya musanta kisan-kare-dangin shekara ta 1994, ya shaida wa Rfi cewa hukumomin Rwandan sun so hallaka shi ne.Furofesan wanda aka mai da shi Amurka Talatar da ta gabata bisa dalilan rashin lafiya, yana kare wani da ake zargi da laifin kasancewa kanwa-uwar-gamin kisan kare-dangin ne, aka kama shi aka tsare tun 28 ga watan Mayu.Ya shaida wa Rfi cewa, wasu mutane shida karfafa sanye da farin kaya ne suka kewaye teburinsa, suka ce ya tashi ya bi su. 

Furofesa Erlinder yayin hira da 'yan jaridu a Nairobin Kenya
Furofesa Erlinder yayin hira da 'yan jaridu a Nairobin Kenya Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.