Isa ga babban shafi
Somaliya

Shebab mai daurin gindin Al Qaeda ta gargadi masu jefa kuri’a a arewacin yankin Somaliland

A yankin Somalia da ya balle, kungiyar Shebab dake samun daurin-gindin Al Qaeda ta gargadi masu jefa kuri’a a kudanci, su kaurace wa zaben shugabancin yankin.Kungiyar ta yi gargadin ne cikin wani sakon-sautin murya da ta aike wa kamfanin dillacin labaran Faransa AFP, inda babban shugaban Shebab din Ahmed Abdi Godane ke cewar wadanda suka kuskura suka shiga wannan zabe da ya kira na jeka-na yi ka, zasu yaba wa aya-zaki.Godane, wanda kuma ake kiransa da Abu Zubayr, kuma haifaffen babban birnin yankin da ya balle wato Hargeisa, ya ce masu adawa da dakarun musulunci a Somalia ne suka shirya zaben.Gobe Asabar za a gudanar da zaben na Somaliland da aka yi ta dage shi har sau uku tun cikin shekara ta 2008, shekaru 50 bayan samun ‘yancin kai daga Birtaniya.  

Wasu daga cikin dakarun kungiyar shebab
Wasu daga cikin dakarun kungiyar shebab AFP / M. Dahir
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.