Isa ga babban shafi
Rwanda

Kotu Ta Daure Tsoho Shekaru 25

Kotun kasa-da-kasa dake bin diddigin kisan kiyashi a kasar Rwanda cikin shekara ta 1994, a yau ta yanke hukuncin dauri na shekaru 25 kan wani tsoho mai shekaru 75 da ake tsare dashi.Ana zargin tsohon ne da kashe dubban mutane.Tsohon, mai suna Yussuf Munyakazi, wanda yake da ‘ya’ya 13, an same shi da hannu dumu dumu wajen kashe mutane daga kabilar Tutsi, wadanda suka sami mafaka a wani cocin Katolika.Bayanai na nuna cewa tsohon ne ya jagoranci mayaka zuwa cocin  ranar 29 ga watan Aprilu, 1994, inda sukayi ta kashe mutane.Shaidu sun fadi cewa shine jagoran mayakan da suka kai hari kan fararen hula da aka hallaka kusan 5,000.Kotun kasa da kasan dake zaman ta a birnin Arusha dake Arewacin kasar Tanzania nada alhakin hukunta dukkan wadan da suke da hannu wajen kisan kiyashin kasar Rwanda.  

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.