Isa ga babban shafi
Uganda

An Fara Taron Kungiyar Tarayyar Afrika

Yau ne aka bude taron Majalisar Ministocin kungiyar kasashen Afrika, a birnin Kampala na kasar Uganda.Wakilinmu dake halartan taron Bashir Ibrahim Idris yace a jawabin bude taron Shugaban Hukumar Gudanarwan Kungiyar Jean Ping yace duk da nasarorin da aka samu wajen magance matsalolin tattalin arziki a duniya, har yanzu akwai sauran rina a kaba musamman wajen samar da ayyukan yi ga dimbin jamaa, kayayyakin more rayuwa, lafiya da kuma ilmi.Jean Ping yace shan kashi da kudin Turai Euro ke sha, na shafar tattalin arzikin kasashen Afrika.Saboda haka ya nemi karin hadin kan kasashen Afrika a cikin gida domin a tafi da murya daya, musamman waje magance mace- macen mata da kuma kananan yara.Shima a nashi jawabin Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Abdullahi Jani yace matsalar mace- macen mata da yara kanana, ba wani abinda zaayi sako sako dashi ne ba.A jawabinta Mataimakiyar Ministan Waje na kasar Japan, Chinama Nashuura ta fadi cewa kasar Japan zata bada tallafin kudade da suka kai Dalan Amirka Miliyan dari biyar don magance mace- macen mata da yara kanana a nahiyar Africa wanda shine taken wannan taron.Tace kasar Japan da Afrika abokai ne sosai.Za’a kwashe kwanaki uku ana wannan taro.  

Shugaban Hukumar Tarayyar Afrika Jean Ping
Shugaban Hukumar Tarayyar Afrika Jean Ping rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.