Isa ga babban shafi
Najeriya

Hukumar zabe a Nigeria ta sanar da jadawalin zabubuka

HUKUMAR Zabe a Nigeria, ta sanar da ranakun da za’a gudanar da zabubbukan shekara mai zuwa daga matakin Jiha zuwa matakin kasa baki daya.Jadawalin da hukumar ta bayar ta hannun kwamishinan ta Solomon Soyebi, ya nuna cewa, za’a gudanar da zaben, shugaban kasa ranar 22 ga watan Janairu, kana kuma za’a gudanar da zaben Gwamnonin Jihohi ranar 29 ga wata.Hukumar tace zata gudanar da rajistar masu kada kuri’u daga ranakun 1 ga watan Nuwamba, zuwa 14 ga wata, inda kuma zata baje kolin rajistar daga 20 ga watan Nuwamba zuwa 25 ga wata.Tuni dai Yan siyasa suka yabada jadawalin, sai dai kuma sun bayyana korafinsu kan lokacin da za’a dauka wajen rajistar masu kada kuri’un, inda suke cewa, ya kasa, ganin yawan mutanen da za’a yiwa rajistar.

Solomon Soyebi
Solomon Soyebi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.