Isa ga babban shafi
NIjar

ECOWAS ta nemi a saki Tandja

A yau Litinin, Kotun kungiyar kasashen yammacin Africa, ECOWAS ta bada umurnin gaggauta sakin tsohon shugaban kasar Nijar Mamadou Tandja wanda gwamnatin mulkin Sojin kasar ke tsare da shi.A fadar shugaban kasar gwamnatin Nijar ne da ke Niamey aka kama Tandja, lokacin da sojoji a kasar suka kifar da gwamnatinsa a 18 ga watan Febrairun shekarar nan wanda hakan ya kawo karshen mulkin sa shekaru bayan kwashe shekaru goma yana mulkin kasar.Kotun dai ta bayyana cewa tsare Tandja ba tare da tuhumarsa da aikata wani laifi ba wani mataki ne na keta hakkinsa na Bil’adama.A shekarar da ta gabata ne Shugaba Tandja ya jefa kasar Nijar cikin rudani a kokarinsa na yin tazarce a kan ragamar mulkin kasar bayan kwashe shekaru biyar sai biyu yana mulkin kasar wanda hakan kuma ya kawo karshen wa’adin mulkinsa.  

Tsohon shugaban kasar Nijar Mamadou Tandja
Tsohon shugaban kasar Nijar Mamadou Tandja
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.