Isa ga babban shafi
Ecowas

ECOWAS zata gudanar da taron gaggawa dangane da rikicin siyasar Ivory Coast

A yau Talata ne kungiyar ECOWAS ta sanar da cewa zata gudanar da wani taron gaggawa juma’a mai zuwa dangane da rikicin siyasar Ivory Coast, bayan dakatawar da ta yi mata daga cikin kungiyar, ta bukaci Laurent Gbagbo ya mika mulki.Kakakin kungiyar mai mambobi 15 ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa Suna so ne su yi nazarin abubuwan dake faruwa a Cote d’ Ivoire, don ganin wace matsaya za su dauka baki daya.Za dai a gudanar da taron ne a babban birnin tarayyar Nigeria Abuja.  

Laurent Gbagbo da Alassane Ouattara dake takaddamar shugabanci.
Laurent Gbagbo da Alassane Ouattara dake takaddamar shugabanci. Montagem RFI / Pierre Moussart
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.