Isa ga babban shafi
Cote d’ivoire

Gbagbo yace zai yi watsi da bukatun ECOWAS

A kokarin da kungiyar kasashen yammacin Africa ECOWAS ke yi wajen ganin shawo kan rikicin siyasar kasar Cote d’Ivoire bayan kammala zaben kasar da aka gudanar, shugaban kasar ta Cote d’Ivoire mai barin gado Laurent Gbagbo yace zai yi watsi da bukatar ECOWAS kan lalle sai ya mika mulki ga abokin hamayyarsa Alassane Ouattara ko kuma ya fuskancin fushin kungiyar.A yanzu haka dai shugaban kasar Kenya Raila Odinga wakilin kungiyar tarayyar Africa na musamman tuni ya isa Abidjan babban birnin kasar inda ake sa ran zai hadu da shugabannin kashen Africa guda uku masu wakiltan ECOWAS inda za su tattauna wajen kokarin shawo kan Laurent Gbagbo ya sauka daga kujerar shugabancin kasar da ya sha kaye a zaben da aka gudanar a watan Nuwamba wanda Duniya kuma ta tabbatar da haka.A yanzu haka sanadiyar rikicin siyasar kasar, mutane sama da 170 ne suka mutu wanda hakan ke bada alamun sake ballewar yakin basasa tun bayan wanda ya taba aukuwa a kasar a shekarar 2002. Shugaba Gbagbo wanda ke fuskantar matsin lamba daga kungiyoyin kasashen turai wadanda suka nemi dole sai ya sauka amman a nasa bangaren shugaban yana tunkaho ne da kotun kasar da ke mara masa baya da kuma rundurar soji. Kusan a karshen makon nan ne shugaban ya soki abokin hamayyarsa Ouattara a kafar yada labaran talebijin cewa kada ya jira kasashen waje su daura shi kan kujerar shugabancin kasar.Sai dai kuma Ibrahim Ben Kargbo mai Magana da yawun shugaban kasar Saliyo daya daga cikin wakilan ECOWAS, ya bayyana cewa shugabannin zasu hurawa Gbagbo wauta sai ya sauka daga kujerar shugabancin kasar don kaucewa barkewar yaki a kasar.  

Laurent Gbagbo tare da Shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma.
Laurent Gbagbo tare da Shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma. © REUTERS/Thierry Gouegnon
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.