Isa ga babban shafi
Nijar

Zaben kananan hukumomin Niger ya hadu da matsala a wasu Jahohi

A yau talata kimanin al’ummar kasar Niger miliyan shida da dubu dari bakwai ne suka fara zaben ‘yan majalisun kananan hukumomin kasar, matakin farko na yunkurin sake maida kasar kan turbar demokradiya da ake yi, bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin farar hula, ta shugaban kasar Tanja Mamadu, a ranar 18 ga watan Fabrairun bara. shugaban mulkin sojan kasar Janar Salu Jibbo ne, ya fara kada tasa kuri'ar a rumfar zabe mai lamba daya, da ke ofishin ma'aikatar Magajin garin birnin Yamai babban birnin kasarda farko dai zaben an shirya yin sa ne a ranar assabar da ta gabata, amma aka daga shi zuwa yau talata, sakamakon matsalar kasa isar da kayyakin zaben a wasu yankunan kasar kan lokaci.Sai dai duk da haka zaben na yau, ya hadu da cikas a wasu jahohin kasar, wadanda suka hada da jahar Maradi da Damagaram, inda aka dakatar da zaben a wasu yankunan jahar Maradi, sanadiyar kasa isar da takardun zaben wasu jam’iyyu siyasa, a yayin da a jahar Damagaram akwatunnan zabe ne aka rasa a wasu mazabun jahar.A cewar Ibrahim Mamman Ilalla na jam’iyar RSD Gaskiya, wannan rashin akwatunan zabe da aka yi, ya nuna cewa, hukumar zaben kasar CNI ta fara saka da mugun zare, ya kuma zama dole ta dauki matakin gaggawa wajen magance matsalar, kafin zuwan manyan zabubbukan da suka hada da na shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki. 

wata mata na kada kuri'arta a kasar Nija
wata mata na kada kuri'arta a kasar Nija
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.