Isa ga babban shafi
Tunisiya

Shugaban kasar Tunisia dai ya tsere daga kasar

Bayan da matsin lamba, zanga-zanga da tashe-tashen hankula sun ta’azzara a kasar Tunisia, kana kuma jawabin da Zine El Abidine ya yi don kwantar da hakali ya kasa canja komai, illa rura wutar ci gaba da zanga-zangar kin jininsa kan tsadar abinci da rashin aiki yi, yanzu dai ya tsere bayan shekaru 23 yana mulkin kasar.Muguwar zanga-zanga da kafsa fada tsakanin masu zanga-zanga da ‘yan sanda kwantar da tarzoma da aka kwashe kwanaki ana yi, ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.Bayan tserewar Zine Al Abidine, Firayi minista Mohammed Ghannouchi ya ayyana kansa a matsayin shugaban gwamnatin rukon-kwaryar kasar tare da kafa dokar Ta-baci, sannan ya bukaci ‘yan Tunisia da su hada kai, yana mai cewa yanzu shi adda ragamar ikon kasar. 

Shugaban Tunisia Zine Al-Abidine yana jawabi gabanin ya tsere ya bar kasar
Shugaban Tunisia Zine Al-Abidine yana jawabi gabanin ya tsere ya bar kasar Reuters/Tunisian State TV/Handout
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.