Isa ga babban shafi
Niger

An fara jefa kuri’a a zaben shugaban kasa a Nijar

A yau litinin al’ummar kasar Jamhuriyyar Nijar sun fara jefa kuri’ar zaben shugaban kasa don neman mayar da kasar ga tafarkin mulkin demokradiyya, bayan da sojojin kasar suka hambarar da gwamnatin shugaba Tandja. Sai dai kuma kafin fara zaben wasu ‘yan siyasa sun yi zargin tafka magudi.

AFP / Boureima Hama
Talla

A lokacin da yake jawabi a karshen mako, shugaban hukumar zaben kasar yace ya samu labarin ana sayar da katin rejistar zabe na bugi tsakanin ‘yan siyasa kafin fara gudanar da zaben, ba tare da bayyana adadinsu, al’amarin da ya sanya wasu daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar guda takwas daga cikin goma suka bukaci a dage zaben domin samun isasshen lokacin shirya gudanar da zaben.

ZABEN KASAR NIJAR

Tuni dai gwamnatin sojin kasar ta yi watsi da wannan bukatar da ke neman sauya lokacin gudanar da zaben, kamar yadda shugaban kasar Salou Djibo ya yi alkawalin sauka daga mulki a watan Aprilu.

A cewar shugaban kasar Salou Djibo bayan jefa kuri’arsa “ ina cikin farin ciki da gamsuwa domin wannan wani sabon tafarki ne ga Jamhuriyyar Nijar, tafarkin da zai bai wa sabbin shugabanni mayar da hankali ga ci gaban kasa”

A watan Fabrairun shekarar bara ne sojoji suka karbi mulkin kasar bayan hambarar da shugaba Mamadou Tandja wanda ya nemi yin tajarce ta hanyar sauya kundin tsarin mulkin kasar.

Daga cikin masu neman kujerar shugaban cin kasar sun hada da madugun ‘yan adawa Mahamadou Issoufou da Seini Oumarou na Jam’iyyar MNSD tsohon Prime Ministan a gwamnatin Tandja da kuma Hama Amadou.

A yanzu haka daruruwan kungiyoyin sa ido ne suka kai ziyara a zaben kasar, wadanda suka hada da kungiyar Yammacin Africa ta ECOWAS da kungiyar tarayyar kasashen Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.