Isa ga babban shafi
SUDAN

Al Bashir ya amince da ‘yancin kudanci

Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Al Bashir ya bayyana amincewarsa ga sakamakon zaben da aka gudanar wanda ke nuna ballewar yankin kudancin kasar a matsayin kasa mai cin gashin kanta. Ana dai dakun sakamkon karshe na zaben a yau litinin amma sakamakon farko ya nuna kashi 98.83 sun amince da ‘yancin kudanci a watan Julin bana.A lokacin da yake jawabi a kafar yada labaran telebijin ta kasar, shugaba Al Bashir yace ya amince da sakamakon zaben jin ra’ayin al’ummar kasar domin shi ne abunda al’ummar yankin kudancin kasar suka amince da shi.Wannan zaben na jin ra’ayin jama’a kan ‘yancin kudanci shi ne dai tabbacin yarjejeniyar zaman lafiya ta 2005 tsakanin yankin kudanci da Arewacin sudan da suka kulla wanda hakan zai kawo karshen rikici da aka kwashe shekaru ana gudanar a kasar.Shugaban yankin kudanci Salva Kiir ya jinjinawa Shugaba hassan Al Bashir kan amincewa da sakamakon zaben tare da cewa shugaban ya cancanci a yaba masa.Sai dai kuma ana hasashen yiyuwar ballewar rikici yayin yankunan biyu suka rabu wajen tafiyar da arzikin kasar musamman man Fetir. 

Shugaban kasar Sudan Hassan Umar Albashir
Shugaban kasar Sudan Hassan Umar Albashir Reuters/Mohamed Nureldin Abdallah
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.