Zamu ci gaba da haramta fita da Cocoa, inji Ouattara
Shugaban kasar Cote d’Ivoire mai jiran gado Alassane Ouattara ya bayyana cewa zasu kara wa’adin haramcin fita da Cocoa daga kasar a matakin da suka dauka tun da farko na tsawon wata guda idan har abokin hamayyarsa Laurent Gbagbo ya ki amincewa ya sauka daga madafan ikon kasar.A wata hira da shugaban ya yi da kafafen yada larabarai, mista Ouattara yace a shirye ya ke ya yi amfani da takunkumi a fannin tattalin arziki domin tursasawa Laurent Gbagbo ban kwana da madafan iko.Alassane Ouattara shi ne dai hukumar zaben kasar ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben kasar da aka gudanar a watan Nuwambar bara, kuma wanda kasashen duniya suka amince da shi a matsayin shugaban kasar Cote d’Ivoire inda kuma Laurent Gbagbo ya ki amincewa ya sauka bayan ya sha kaye a zaben.A 23 ga watan Janairun bana ne Mista Ouattara ya haramta fita da Cocoa a kasar na tsawon wata daya inda a yanzu yake tunanin ci gaba da wannan matakin domin kawo karshen takaddamar ja-in-jar shugabanci tsakaninsa da Laurent Gbagbo.
Wallafawa ranar: