Isa ga babban shafi
Uganda

Ana Gudanar da zaben shugaban kasar Uganda

Ana gudanar da zabe shugaban kasa da 'yan majalisun Uganda, amma akwai matsalar rashin isassun kayan aiki a wasu mazabun da ‘yan adawa ke da karfi dake Kampala babban birnin kasar.Rashin kayan aikin ya fara fitowa fil da kokawar da ‘yan adawa ke yi ne cewa shugaba Yoweri Musaveni da ya kwashe shekaru 25 ya na mulkin kasar ya shirya tafka magudi.Tuni kakakin hukumar zaben kasar ta Uganda ya daura alhakin rashin kaya aikin kan matsalar chunkoson motoci a kan hanya.Madugun ‘yan adawa Kizza Besigye ya nemi gudanar da zanga zanga salon wadda ta kawo karshen wasu gwamnatocin kasashen Larabawa muddun a ka samu magudi yayin zaben na yau Jumma’a.Akwai kungiyon saka ido kan zabe na kasashen duniya dake kasar Uganda, domin tabbatar da ganin abun da ke faruwa.

Masu zaben kasar Uganda
Masu zaben kasar Uganda Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.