Isa ga babban shafi
Cote d’ivoire

Lamura na kara dakulewa a kasar Cote d'Ivoire

Matasa Magoya bayan shugaba Laurrent Gbagbo na kasar Cote d’Ivoire, sun kai hari gidajen manyan jami’an Alassane Ouattara, a dai dai lokacin da ake samun sabon tashin hankali a kasar.Shaidun gani da ido, sun ce magoya bayan Gbagbo na cig aba da sace kayayaki a gidajen jami’an Ouatara, yayin da jami’an tsaro ke zuba ido. Rohotanni sun nuna yadda matasan ke cinna wa wasu gidaje wuta.Kasashen duniya na bayyana damuwarsu kan barkewar yakin basasa a cikin kasar ta Cote d'Ivoire, bayan zaben watan Nowamban shekarar data gabata, wanda duniya ta hakikance Alassane Ouattara ya lashe.A wani labarin 'yan tawayen kasar sun bayyana sake kwace wani gari Toulepleu daga hanun dakaru masu biyayya wa Gbagbo. 

Birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire
Birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.