Isa ga babban shafi
Libya

Kasashen Duniya na shirin tabbatar da takunkumi kan Libya

Akalla mutane 25 sun hallaka yayin karawa tsakanin masu bore da dakarun sojan kasar Libya a birnin Misrata, kamar yadda rohotanni suka tabbatar.Wannan bayan gwamnatin Muammar Gaddafi ta aiyana tsagaita wuta nan take, sakamakon kudirin MDD da ya nemi haka, ko kuma ayi anfani da karfi, saboda haramta kara kainan jiragen sama da Kwamitin Sulhun MDD ya yi.Shugaban Amurka Barack Obama ya nemi dakarun Libya su janye tare da daina kai farmaki, idan kuma suka yi kunnen kashi lallai kasashen dunioya zasu aiwatar da kudirin MDD. Gwamnatin kasar ta Libya tab akin Ministan harkokin waje Moussa Koussa ta bayyana biyayya wa kudirin na MDD tare da cewa ta daina kai farmaki.Shugabannin kasashen Amurka, Birtaniya, Faransa da kasashen Larabawa na shirin gudanar da taro a Paris babban birnin kasar Faransa, domin daukan matakan aiki da kudirin MDD wanda ya haramta shawagin jiragen sama a sararin samaniyar Libya, da tsagaita wuta kan hare haren gwamnati kan masu bore. 

Reuters/Suhaib Salem
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.