Isa ga babban shafi
Libya

Ministan harkokin wajen Libya Koussa ya sauya sheka

Rohotanni daga Kasar Libya, sun ce dakarun shugaba Muammar Ghaddafi, sun tilastawa 'yan tawayen kasar, janyewa daga garuruwan Ras Lanuf, Bin Jawad da Brega, yayin da ake ci gaba da barin wuta tsakanin bangarorin biyu.Ministan harkokin wajen kasar ta Libya Moussa Koussa ya sauya sheka daga bangaren Gaddafi, inda yanzu haka ya ke birnin London na kasar Birtaniya.Rohotanni daga kasar, sun ce kasahsen Amurka da Birtaniya, sun tura jami’an leken asirinsu kasar Libya, dan ganawa da 'yan tawayen dake dauke da makamai.Fadar shugaban Amurka taki cewa komai dangane da rahotan, da kuma bayanan cewa, shugaba Obama ya amince da wata dokar aikin jami’an leken asirin Amurka a cikin kasar ta Libya.Shugaban kula da shigi da fice na kungiyar kasahsen Turai, Cecilia Malmstrom, ta bukaci kungiyar da ta taimaka wajen magance matsalar bakin haure a kasashen dake Arewacin Afrika.Malmstrom tace ya zama wajibi su taimakawa Yan gudun hijirar dake gujewa tashin hankalin da ake a kasar Libya.Kungiyar Tsaro ta NATO, ko kuma OTAN, yau ta karbi ragamar tafi da hare haren da ake kaiwa kasar Libya, daga hannun kasashen Yammacin duniya, a dai dai lokacin da dakarun shugaba Muammar Ghaddafi ke ci gaba da kora 'yan tawaye baya. 

Moussa Koussa
Moussa Koussa رویترز
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.