Isa ga babban shafi
Libya

Dole Gaddafi ya sauka, inji kasashen duniya

A wata ganawa da ta hada kasashen larabawa da na yammaci a kasar Qatar domin kawo karshen rikicin kasar Libya, wakilan kasashen sun jaddada cewa lalle sai Shugaban kasar ya yi bankwana akan madafan ikon kasar. Duk da cewa babu wani sahihin mataki da aka cim ma kan tunbuke shugaban.A jiya laraba ne ministocin kula da harakokin wajen kasashen Turai da na yankin Gabas ta tsakiya suka gana a Qatar inda suka amince da kawo karshen mulkin shugaban Muammar Gaddafi.Sakataren majalisar Dunkin Duniya Ban Ki-moon da Catherine Ashton ta kungiyar Tarayyar Turai da Amr Moussa na kungiyar Kasashen Larabawa da kuma wasu wakilan kungiyar Tarayyar Africa zasu hadu a Birnin Al Qahira domin tattauna rikicin kasar ta Libya.Ban Ki-moon ya yi gargadin cewa miliyoyan ‘yan kasar Libyasuna bukatar ceto, al’amarin day a bayyana cewa rabin ‘yan kasar sun kaura daga kasar tun faruwa rikicin. 

Jekadan Britaniya kan harakokin kasashen waje a bangaren dama tare da Sarki Tamim Bin Hamad na Qatar
Jekadan Britaniya kan harakokin kasashen waje a bangaren dama tare da Sarki Tamim Bin Hamad na Qatar Reuters/Mohammed Dabbous
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.