Isa ga babban shafi
Najeriya

Masu saka ido sun yaba da zaben Shugaban kasa na Najeriya

Masu sa ido a zaben Nigeria, sun yaba da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasar, a karshen mako.Tsohon shugaban kasar Botswana, Festus Mogae, wanda ya sanya ido a zaben ya bayyana cewa mamaki kan yadda aka gudanar da zaben, ganin yadda kasar ta yi kaurin suna wajen magudin zabe, musamman zaben shekarar 2007, wannan karon mutanen kasar sun zaku wajen ganin an gudanar da zaben yadda ya kamata.Masana harkokin tsaro na bayyana cewa muddun aka ci gaba da inganta hanyoyin zabe zasu taimaka wajen magance matsalolin tsaro da kasar ta Nigeria ke fuskanta.Jam'iyyar adawa ta CPC dake tarayyar ta Nigeria, ta yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a karshen makon. Sakataren jam’iyar, Buba Galadima, ya bayyana korafinsu akai.HUKUMAR Zabe a Nigeria, ta bukaci duk masu zargin cewar anyi magudi da su gabatar mata da hujjar yin haka.

Masu saka ido a zaben Najeriya
Masu saka ido a zaben Najeriya
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.