Chadi
Yan kasar Cadi masu gudun hijira kan zaben kasar
Zaben shugaban kasar Cadi da aka gudanar jiya Litinin, ya nuna shugaba Idriss Deby zai samu nasara karo na hudu, bayan ‘yan adawa sun kauracema zaben.Mafiyawancin mazabu sun kasance wayam, amma kawo yanzu babu adadin wadanda suka fita jifa kuri’un na su ,daga cikin masu zabe mutane milyan biyar.Idrissa Deby Itno ya na mulkin kasar ta Cadi tun bayan juyin mulkin shekarar ta 1990.Tuni tsaffin kungiyoyin ‘yan tawaye da ke gudun hijira a wajen kasar suka yi watsi da sakamakon zaben, kamar yadda Kanal Jibrin Ibrahim tsohon dan tawaye ke cewa.
Wallafawa ranar: