Isa ga babban shafi
Najeria

An kashe wani Hakimi a Maiduguri a Najeriya

‘yan sanda a Najeriya sun tabbatar da mutuwar wani hakimi a Jahar Maiduguri a Nigeria, wanda ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka bindige shi tare da jikkata wani mutum daya.Hakimin mai suna Abba Mukhtar, an bayyana cewa wasu ne a saman Babur su biyu dauke da bindiga suka bude masa wuta a kofar gidansa, kamar yadda kakakin ‘yan sandan jahar Lawal Abdullahi ya sanar.Ana dai zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kai harin. A watannin da suka gabata kungiyaur ta kai hare hare ga gidajen Sojoji da ‘yan sanda da gidajen ‘yan siyasa musamman kisan wani dan takara mai neman kujerar gwamnan jahar Maiduguri.A yanzu haka dai zababben gwamnan jahar Maiduguri Kashim shettima ya bayyana fatarsa na neman zaunawa da ‘yan Boko haram a teburin shawara domin kawo karshen hare haren. Sai dai kungiyar ta Boko Haram ta yi watsi da yunkurin na sabon gwamnan. 

Kofar Shiga Birnin Maiduguri Jahar Borno a Tarayyar Najeriya.
Kofar Shiga Birnin Maiduguri Jahar Borno a Tarayyar Najeriya. RFI / Julie Vandal
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.