Isa ga babban shafi
Masar

Masar : cin hanci da binciken tsohin hukumomin kasar

Matar tsohon shugaban kasar Masar Hosni Mubarak Suzanne Tabet, ta bayyana aniyarta na mika gabadayan dukiyar da ta mallaka ga gwamnatin kasar, yan kwanaki bayan da aka yi mata tsaron wucin gadi a karkashin binciken da ake yi mata na tara dukiya a karkashin cin hanci, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Mena ya sanar.Suzanne Tabet yar shekaru 70 a duniya na ci gaba da karbar magani a wani asibitin garin Sharm El Cheikh inda aka kwantar da ita a ranar juma’ar da ta gabata, bayan da ta kamu da cutar bugun zuciya.  

Suzanne Moubarak
Suzanne Moubarak AFP PHOTO / FETHI BELAID
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.