Libya
Ministan man fetur na Libya ya tsallaka zuwa Tunisiya
Ministan kula da harkokin man fetur na kasar Libya, Shukri Ghanem ya zama jami’i na baya baya da ya fice daga cikin gwamnati Muammar Gaddafi mai fuskantar tawaye.Jami’an kasar Tunisya sun bayyana cewa jami’in Ghanem wanda tsohon PM kasar ta Libya ne, ya tsallaka kan iyaka ta mota.Gwamnatin kasar ta Libya ta bayyana cewa jami’in ya na tafiya ce a hukumance, amma ta daina jin duriyarsa daga bisani.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: