Isa ga babban shafi
Sudan

Dubban Mutane sun Tsere daga rikcin yankin Abyei na kasar Sudan

Kasashen duniya na ci gaba da sukar, mamayen da dakarun kasar Sudan suka yi wa yankin Abyei, dake kan iyakar kudanci da arewacin kasar Sudan.Dubban fararen hula ne daga yankin kudanci ke ci gaba da tserewa yankin na Abyei da ake ja in ja a kansa tsakanin kudanci da arewacin kasar ta Sudan, bayan da a ranar Asabar dakaru da tankokin yakin gwamnatin Sudan sun mamaye shi. Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa fiye da mutane 15,000 suka tsere daga rikicin kawo yanzu.Tawagar MDD a kasar ta yi tir da tashin hankalin tare da kwasar ganimar da dakarun Gwamnatin Sudan ke yi a yankin, inda da neman mahukumtan kasar da su kawo karshen aikata rashin gaskiyar dake wakana.Shi dai Yankin Abei ya kasance daya daga cikin yankunan da ke kashin bayan rikici a kasar ta Sudan tun 2005, lokacin da aka kawo karshen yakin basasar kasar, tsakanin Arewaci Musulmi da kuma na Kudanci da mafi yawansu Cristoci ne.Rikicin dai ya shafi kokarin mallakar ruwan dake gurin ne, wanda ya samo asali daga da dadaddiyar gabar da ake yi tsakanin kabilun biyu.Kasar Amurka ta nemi gwamnatin Sudan da ta gaggauta ficewa daga yankin, da ta mamaye a matsayin taka dokokin duniya, a yayin da mahukumtan kasar ta Sudan kuma, suka bayyana ci gaba da rike yankin har sai an kammala cimma sabuwar yarjejeniyar tsaro a tsakaninsu. 

Abyei
Abyei Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.