Libya
NATO ta zafafa hare haren kan birnin Tripoli na LIbya
Karfafan fashe fashe sun ratsa Tripoli babban birnin kasar Libya, kusa da gidan shugaba Mu’ammar Ghaddafi, sakamakon hare haren da kungiyar kawacen Tsaro ta NATO ke ci gaba da kaiwa, ba tare da kaukautawa ba.Wani shaidar gani da ido, ya shaidawa kanfanin Dillancin labaran Faransa cewar, sun ji karar fashe fashe shida, yayin da jiragen yaki suka yi shawagi a sararin samaniyar kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: