Africa ta kudu
Shugaban Afrika ta Kudu Zuma zai gana dana Libya Gaddafi
Rohotanni daga kasar Afrika ta kudu, sun ce shugaba Jacob Zuma, zai je kasar Libya makon gobe, dan tattauna yadda shugaba Mummar Ghadafi zai bar karagar mulki, yayin da kungiyar kawancen NATO ko OTAN ke ci gaba da kai hare hare kan Tripoli babban birnin kasar.Ranar Litinin ake saran Zuma zai kai ziyarar, kamar yadda sanarwar gwamnatin kasar ta Afrika ta Kudu ta bayyana. Manyan kasashen duniya, sun kekashe kasa sai sun raba Gaddafi da karagar mulki, yayin da shugaban ke cewa ba zai sauka ba, bayan mulkin shekaru 42.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: