Isa ga babban shafi

Duk da hare-haren NATO Kadafi ya ce babu maganar sabka daga kojerar mulkin kasar Libiya

Shugaban Kasar Libiya, Muammar Ghadafi, ya sake jaddada matsayin shi na cewar, ba zai sauka ba daga kan karagar mulkin kasar.Shugaban ya zargi rundunar tsaro ta NATO da kai hare-hare sau 60 a jiya, inda suka kashe mutane 31.A wata hira da aka yadda ta kafofin labarai, shugaba Ghadafi ya ce, an kai harin kusa da inda yake, amma ba zai bada kai bori ya hau ba.Jakadan kasar Rasha da ya ziyarci kasar, Mikhail Mergelov, ya ce a shirye suke su sasanta.Inda ya ke kalamai kamar haka:‘Muna goyan bayan warware matsalar ta hanyar siyasa, ba wai ci gaba da kai hare- hare ba, Rasha a shirye take wajen taimakawa, ta kowace hanya, a matsayin kamar mu ta wakiliyar kwamitin Sulhu da kuma kungiyar G-8.’ 

Turnikewar hayaki bayan hare-haren NATO a Tripoli kasar Libiya
Turnikewar hayaki bayan hare-haren NATO a Tripoli kasar Libiya AFP/STR
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.