Libya
'Yan tawayen Libya sun sha al'washin ci gaba da kwangilolin mai da Kadhafi ya faro
‘Yan tawayen kasar Libya sun ce za su aiwatar da duk wata yarjejeniyar da a aka kulla da Gwmnatin shugba Kadhafi, kan kwangilolin harkar man fetur din kasar. Kamfanonin mai daga kasashen Italy da Norway ne ke gudanar da harkokin tonon mai a kasar, tare da kamfanin NOC na kasar ta Libya, sai dai kuma fadan da ake yi a kasar ya jawo an dakatar da hakar. Kasar Libya ce ke da a kalla kashi 5 cikin 100 na dukkan man fetur din da ake samarwa a duniya.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: