Libya
Faransa ta karyata cewa tana tattaunawa da mahukuntan kasar Libya
Kasar Faransa ta musanta tattaunawa ta kai tsaye da gwamnati Shugaban Libya Muammar Gaddafi, amma tace ta bukaci mahukuntan Tripoli suyi ban kwana da madafun iko, domin samun zaman lafiya.Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Faransa Bernard Valero ya bayyana cewa kamar kullum kasar Faransa ta neman hanyoyin siyasa, domin magance rikicin.Martanin ya biyo bayan wasu kamalan dan shugaba Gaddafi, Saif al-Islam wanda ya shaida wa wata jaridar kasar Algeria, cewa gwamnati tana tattaunawa da Faransa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: