Isa ga babban shafi
Africa

Bunkasa masana'antu ne kawai zai yaki talauci a Africa

Wani Binciken Majalisar Dinkin Duniya, ya nuna cewar dole sai kasashen Afrika sun bunkasa harkar masana’antu kafin suyi yaki da talauci.Rahotan, wanda ya bayyana cewar nahiyar Afrika na bada gudumawar kashi daya ne kawai na masa’antun duniya, yayin da Asia ta tashi daga bada gudumawar kashi 13 daga shekarar 2000 zuwa kashi 25 a shekarar 2008.Rahotan ya danganta cigaban da kasashen Asia da China suka samu, da cigaban masana’antu, abinda ke samun koma baya a nahiyar Afrika, wanda ke da dimbin arzikin ma’adinai da anfanin gona. 

Synutra
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.