Isa ga babban shafi
Kenya

Shugaban Kenya ya kone hauren giwaye

Shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki da hannunsa a birnin Nairobi ya kyasta wuta kan tarin hauren giwa samada ton biyar, domin shagulgulan bukin ranar aiki da dokokin kare hakkin Giwaye.Shugaba Kibaki ya kona hauren giwaye 335, sannan ya sake kyasta wuta kan wasu sassaka da akayi da hauren giwa guda dubu 40, wadanda aka kwace daga hannun masu fasa kwauri zuwa kasar Singapore.Bayanai na nuna cewa a shekarar data gabata jimillar giwa 187 aka kashe ba bisa kaida ba a dazukan kasar, ko dai don cin naman su, ko kuma fataucin wasu sassan su zuwa wasu kasashe. 

Giwaye na fuskantar barazana a Kenya
Giwaye na fuskantar barazana a Kenya Peter Lillie/Getty Images
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.