Isa ga babban shafi
Libiya

Za ayi binciken kashe kwamandan 'yan tawayen Libiya

Rundunar ‘yan tawayen kasar Libya ta kafa wani kwamitin da zai biciki yadda aka kashe kwamandan ‘yan tawayen, General Abdel Fatah Yunis, da ke kokarin kawar da gwamnatin shugaba Gadafi.Mai kula da lamuran tattalin arziki na bangaren ‘yan tawayen, Ali Torhuni yace za a wallafa dukkan bayanan da aka gano yayin binciken.Ya ce an gano gawar Yunis, da ta sha harsasai, aka kuma kone ta a wani filin da ke tsakanin kauyukan da ke gewaye da yankin bengazi, kuma tuni wanda ya jagoranci masu aika aikar, ya amsa laifin shi. 

Wasu daga cikin 'Yan tawayen kasar Libya
Wasu daga cikin 'Yan tawayen kasar Libya Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.