Libya
An nuna hoton hoton Bidiyon Khamis Gaddafi
Gidan Telebijin din kasar Libya ya nuna hoton bidiyon Dan Mu’ammar Gaddafi Khamis da ‘yan tawayen kasar suka ce sun kashe a makon jiya bayan wani hari da NATO ta kai a Zliten.Tuni dai gwamnatin Libya ta musanta rehotannin da ke cewa Khamis daya daga cikin Kwamandojin yakin Gaddafi ya mutu.Gidan Telebijin din kasar Libya yace an dauki hoton bidiyon ne a jiya Talata wanda hakan ke nuna cewa Khamis Gaddafi na nan da ransa.Hoton Bidiyon dai ya nuna Khamis Gaddafi sanye da kaki da hullar soja akansa.
Wallafawa ranar: