Isa ga babban shafi
Janhuriyar Demokaradiyar Congo

Kabila zai yi takara a matsayin indipenda

A gobe Lahadi aker sa ran shugaban kasar JD Congo President Joseph Kabila zai mika takardar shi ta neman sake tsayawa takarar shugabancin kasar. Zai dai tsaya takara ne a matsayin dan takaran indipenda, duk kuwa da cewa jama’iyyar shi ta PPRD ta tsayar da shi a matsayin da takarar ta.Mai Magana da yawun jama’iyyar yace an dauki wannan matakin ne saboda akwai jama’iyyun kasar fiye da 170 da ke goya mishi baya.Mai shekaru 40, Kabila ya dare karagar mulkin kasar ne a shekarar 2001, bayan da aka yi wa mahaifin shi Laurent Kabila kisan gilla. 

Joseph Kabila shugaban kasar Janhuriyar Demokaradiyar Congo
Joseph Kabila shugaban kasar Janhuriyar Demokaradiyar Congo
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.