Isa ga babban shafi
Masar

Muslim Brotherhood ta yi gargadin kauracewa zaben Masar

An fara samun kalubale a zaben farko da za’a gudanar tun bayan hambarar da Hosni Mubarak a Masar, inda gamayyar Jam’iyyu karkashin jagorancin Muslim Brotherhood suka yi gargadin kauracewa zaben ‘yan Majalisu.Wata Sanarwa da Jam’iyyun suka fitar, sun ce zasu kauracewa zaben Watan Nuwamba na ‘Yan Majalisu idan har ba a sauya kundin tsarin dokokin zaben ba dake da nasaba da tsohuwar gwamnatin Hosni Mubarak.Gamayyar Jam’iyyun ta hada jam’iyyu da dama da suka hada da Jam’iyyar Muslim Brotherhood da Jam’iyyar Liberal Wafd.A ranar 28 ga watan Nuwamba ne gwamnatin rikon kwarya ta Sojin kasar suka bayyana cewa za’a gudanar da zaben ‘Yan Majalisu. 

Wata mai goyon bayan Jam'iyyar Adawa ta Muslim Brotherhood a birnin Al kahira
Wata mai goyon bayan Jam'iyyar Adawa ta Muslim Brotherhood a birnin Al kahira Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.