Isa ga babban shafi
Cote d’ivoire

Cote d’Ivoire zata hannuntawa ICC wadanda aka sumu da hannu a rikicin kasar

Prime Ministan Cote d’Ivoire Guillaume Soro yace gwamnatinsu a shirye take ta hannuntawa kotun hukunta manyan laifuka ta ICC wadanda aka kama da hannu a rikicin da ya biyo bayan kammala zaben shugaban kasa.A hira day a yi da RFI, Guillaume Soro yace zasu bai wa hukumar damar gudanar da bincike a cikin kasar.A cewar Majalisar Dunkin Duniya, mutane 3,000 aka kasha a watanni hudu da aka kwashe ana gwabza fada tsakanin magoya bayan shugaba Ouattara da Laurent Gbagbo wanda ya ki sauka bayan ya sha kaye a zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Nuwambar bara. 

Prime minista Guillaume Soro tare da président Alassane Ouattara, na Cote d'Ivoire
Prime minista Guillaume Soro tare da président Alassane Ouattara, na Cote d'Ivoire ISSOUF SANOGO / AFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.