Sudan
Zanga-zangar tsadar rayuwa a Sudan
Daruruwan al’ummar kasar Sudan ne suka yi gangami a birnin Khartoum a wata zanga-zanga ta adawa da hauhauwan farashin abinci tare da bukatar ingantaccen tsarin Sufuri.Masu zanga-znagar sun fusata ne da matsalar tattalin arzikin kasar bayan samun ‘yancin kudanci da ya haifar da katsewar yawancin albarkatun man Fetir a kasar.A kasar Sudan ana fama da matsalar tsarin Sufuri na gwamnati inda al’ummar kasar suka dogara da kananan motocin haya domin cim ma bukatunsu
Wallafawa ranar: