An yi Jana’izar Gaddafi a asirce a Libya
Hukumomin gwamnatin wuccin gadin Libya sun sanar da yin Jana’izar tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi a asirce, a wani kabarin da aka kebe a yankin Sahara domin kawo karshen takaddamar da ta biyo bayan nuna gawarsa a bainar jama’a.A ranar Alhamis makon jiya ne dakarun ‘yan tawaye suka kashe Gaddafi tare da girke gawarsa mutane na zuwa kallo inda takaddama ta kaure akan yadda zasu yi da gawar tsohon shugaban da aka kwashe watanni ana yakin kawo karshen mulkinsa.Tun da farin dai gwamnatin wuccin gadi ta bukaci ‘yan kabilarsa a mahaifarsa a birnin Sirte wurin da suke ganin ya dace a binne tsohon shugaban domin kaucewa mayar da kabarinsa wajen Ibada.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: