Isa ga babban shafi
Tunisiya

Rikici ya barke a Tunisia bayan zaben ‘Yan Majalisu

Rikici ya barke a Sidi Bouzid tsakiyar birnin Tunisia bayan bayyana sakamakon zaben farko na ‘Yan Majalisu da aka gudanar bayan hambarar da gwamnatin Zine Al Abidine Ben Ali.‘Yan sanda a kasar sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye ga daruruwan masu zanga-zangar adawa da soke zaben kujerar majalisa da wata Jam’iyya ta lashe a Sidi Bouzid.Birnin Sidi Bouzid shi ne cibiyar zanga-zangar da ta barke ta adawa da gwamnatin Zine el Abidine Ben Ali.Sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Lahadi ya nuna Jami’iyyar Musulunci ce ta Ennahda ke da rijayen kuri’u kashi 41 na kuri’un da aka kada, kuma wannan ne ya bata damar samun kujeru 90 cikin kujeru 217 na ‘Yan majalisun kasar 

Masu zanga-zanga a birnin Sidi Bouzid tsakiyar Tunisia
Masu zanga-zanga a birnin Sidi Bouzid tsakiyar Tunisia Kahouli / AFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.