‘Yan Majalisa sun juya wa Jonathan baya a Najeriya
Yunkurin shugaban Najeriya Gooodluck Jonathan na kokarin sasantawa da Majalisar kasar domin neman amincewarsu ga shirinsa na janye tallafin man Fatir ya gamu da cikas bayan da aka tashi baram-baram a zaman taron shugaban da ‘Yan majalisun.
Wallafawa ranar:
Hon Ado Alhassan Doguwa
Jonathan ya kira taron gaggawa ne domin ganawa da Sanatoci 109 da ‘yan majalisar wakilai 360 a fadarsa domin tattauna muhimmacin janye tallafin man Fetir, tare da tattauna hanyoyin magance matsalar tsaro musamman rikicin kungiyar Boko Haram.
An samu sabani ne dai bayan da shugaban ya bayyana cewa shirin janye tallafin Man Fetir shi ne mafita ga Najeriya. Daga nan ne kuma ‘yan majalisun suka fara shewar kin amincewarsu.
Sen Ali Ndume
A lokacin da yake jawabi kakakin majalisar wakilai Aminu Waziri Tambuwal yace Majalisar zata taimaka wajen shawo kan matsalar tsaro a cikin kasar amma sauran bukatun shugaban sai majalisa ta koma zauren muhawararta kafin su dauki matsayi akai.
Gayyatar ta shugaban na zuwa ne bayan da wasu mambobin majalisar suka fara barazar kada kuri’ar tsige shugaban saboda halin matsalar tsaro a Najeriya.
Hon. Yusuf Bala
Yanzu haka kuma ‘Yan majalisun sun juyawa shugaban baya sai dai ministan yada labaran kasar Labaran maku yace gwamnatin zata ci gaba da tattaunawa da ‘yan majalisun domin neman amincewarsu.
Kalaman Labaran Maku, Ministan yada labaran Nigeria
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu