Isa ga babban shafi
Libya

'Yantawaye sun samu mukaman Gwamnati a Libya

‘Yan Tawayen da suka taimaka wajen hambarar da Tsohon shugaban kasar Libya, Muammar Ghaddafi, sun samu mukaman gwamnati daban dabam a sabuwar Gwamnatin kasar bayan sun yi barazanar gudanar da zanga-zangar kifar da gwamnatin.

Fira Ministan kasar Libya El Keib tare da Abdul Hafez Goga a taron manema labarai birnin Tripoli
Fira Ministan kasar Libya El Keib tare da Abdul Hafez Goga a taron manema labarai birnin Tripoli REUTERS/Mohammed Salem
Talla

Fira Ministan riko, AbdelRahim al Kib, ya nada Osama Julli, kwamandan ‘Yantawayen wanda ya kama Saif Islam, a matsayin Ministan tsaro, yayin da Fawzi Abdelali daga Misrata, aka nada shi mukamin Ministan cikin gida.

Tsohon Jakadan Ghaddafi a Canada, wanda ya koma bangaren ‘Yantawayen an biya shi ne da mukamin Ministan harakokin wajen kasar.

Tun da farko dai ‘Yantawayen sun yi barazanar kifar da sabuwar gwamnatin idan har ta yi kokarin bayar da su saniyar ware. Sai dai Fira Ministan kasar yace sun yi kokarin bayar da mukaman gwamnatin ne ga sassan yankunan kasar domin samun wakilci a sabuwar gwamnatin.

A ziyarsa birnin Tripoli mai gabatar da kara a kotun hukunta manyan Laifuka ya amince a gurfanar da Seif al Islam a Libya sabanin yadda kotun ta bukata da farko a birnin Hague.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.